Kannywood

Ina Bawa ‘Yan Uwan Marigayi Kamal Aboki Shawara Da Su Gogé Shafukan Shí Ná Facébook, Tìktók, Instagram,

Ina Bawa ‘Yan Uwan Marigayi Kamal Aboki Shawara Da Su Gogé Shafukan Shí Ná Facébook, Tìktók, Instagram, YouTubé Da Saúran Kafofin Sada Zumunta Da Yaké Da Alaka Da Sú

DÁGA Comr Abba Sani Pantami

Hakika Kamal ya samu kyakkyawar shaida a wurin dubunnan mutanen da yake mu’amala dasu, hakan abun farin ciki ne babba kuma kowa yana burin samun kyakkyawar shaida a lokacin da ya koma ga mahaliccin shi.

Wata kila wayarshi ta shiga hannun ‘yan uwanshi, ina mai rokon su Don Allah da su taimaka su goge dukkannin shafukan shi da YouTube Channel din shi saboda wasu ‘yan dalilai kamar haka;

Na farko a wannan lokacin mutane da dama suka fara sanin wanene shi wasu da dama suna ta shiga shafukan shi na Facebook, TikTok, Instagram da YouTube da sauran su, domin ganin bidiyoyin da yayi na tsawon shekaru wanda duk wani maison shi da gaske bazaiso hakan ba.

Abu na biyu matukar aka yi kokarin goge shafukan shi na tabbata bidiyon shi da dama zasu bata ba za’a sake ganin su ba, madadin ba’a goge shafukan ba.

Abu na uku munsan da cewa koda kuskure guda mutum yayi a duniya, bai kamata bayan mutuwarshi a dinga ganin kuskuren har ana tunawa dashi ba da sauran wasu dalilai wanda basai na zayyano su ba.

Don Allah, Don Allah, Don Allah ina mai rokon makusantan shi dasu taimaka suyi aiki da wannan shawarar tawa.

Hakika Kamal Aboki yana daya daga cikin matasan da suke burgeni musamman a bangaren nishadantarwa ina matukar kaunarshi shiyasa nike bawa ‘yan uwanshi wannan shawarar, ina fatan kuma zaku fahimce ni.

Allah ya jikan Kamal, muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

www.sarkiloaded.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button