Labaran Duniya

Bidiyon Yadda Aka Kama Mijin Daya Daure Matarsa Tsawon Watanni Yana Azabtar Da Ita

Yadda Aka Kama Mijin Daya Daure Matarsa Tsawon Watanni Yana Azabtar Da Ita

A  halin yanzu dai wata matar aure, Sadiya Salihu mai shekara 33 a duniya na can rai kwakwai mutu kwakwai da aka ceto bayan mijinta ya daure ta tsawon watanni.

Sadiya, wadda matar wani dan kasuwa ce da ke Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe, Ibrahim Yunusa Bature, an ruwaito cewar ya daure ta na tsawon watanni cikin mawuyacin halin da a yanzu take fama da matsananciyar rashin lafiya.

Majiyarmu Aminiya ta ruwaito cewa, matar tana can kwance a wani aibitin kudi da ke Unguwar Sheka ta Gabas a Karamar Hukumar Kubutso da ke Jihar Kano.

Matar mai ’ya’ya hudu ta auri mijin nata a ranar 24 ga watan Afrilun 2010, a Unguwar Sheka ta Gabas sannan aka kai ta zaman aure garin Nguru da ke Jihar Yobe.

Bayanai sun ce mijin nata dan asalin Jihar Borno ne, amma yana zaune a Jihar Yobe.

Yayin da Aminiya ta tattauna da mahaifiyarta mai suna Hadiza Hassan, ta ce ta dauko ‘yarta ce bayan ta kai mata ziyara kuma ta yi kicibus da ita a cikin wannan mawuyacin hali da “azzalumin mijin nata ya saka ta a ciki.”

Ta bayyana cewar sakamakon munanan mafarke-mafarke da ta dinga fama da su ne a kan ’yar, ya sa ta tafi garin ba tare da ta shaida wa kowa, wanda da tuni rai ya yi halinsa ba tare da ta sani ba.

Na jima ina yin munanan mafarke-mafarke game da Sadiya, amma duk lokacin da na kira mijinta a waya sai ya hada ni da yara mu gaisa su yi min karya, su ce tana barci ko wani abu daban dai.

Daga karshe, na yanke hukunci na tafi da sassafe zuwa Nguru ba tare da na sanar da kowa ba.

Da zuwana muna gaisawa da yaran abin da na fara yi shi ne na kutsa kai cikin dakinta, nan na tsince ta cikin mawuyacin halin da bukatar taimakon gaggawa.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka.

Www.sarkiloaded.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button