Career

Maganin Gyaran Nono Ta Hanyar Amfani Da Matakai Na Likitancin Zamani

Maganin Gyaran Nono Ta Hanyar Amfani Da Matakai Na Likitancin Zamani

Hanyoyin da mata suke amfani da su wajen gyaran nono (watau karin girmansa da kuma tsayuwarsa) sune:

  1. Kawayoyin magani (breast enhancement pills)

wadannan sune kwayoyin maganin da aka sarrafa su a likitance (pharmaceutical drugs), kuma sune ake kira vitamin supplements.

Mata a cikin wannan group din suna yawan tambaya akan ingancinsu. Kwayoyin suna dauke ne da sinadarin estrogen wanda yake kara girman nono.

Sauran abubuwan da ake sanyawa sun hada da barley (sha’ir), fenugreek (hulba), oats (hatsi), palmetto (dabino), dong quai (wani itace ne da ake samunsa a China), blessed thistle, pueraria mirifica, fennel seed, hops, bovine ovary extract (duka ban san sunayensu da hausa ba).

Bincike ya tabbatar da cewa kwayoyin kara girma da kuma tsayuwar nono suna da illa, musamman idan an dade ana amfani da su. Misalin wadanddan kwayoyi sune Lady Capsule, Bust Maxx, Curves Capsules, Curvinexx, Pueraria Mirifica 3000, Natural Pueraria Mirifica, IsoSensuals Enhance da sauransu.

  1. Mayukan shafawa (breast enhancement creams)

wasu daga cikin ire-iren wadannan mayuka sune Divine Derriere Breast and Butt Enhancement Cream, COS Naturals Breast Plumping Lotion, NanoMed Finale Bust Cream, Diva Fit N’ Sexy Breast Cream, True Level Breast Plumping Lotion, Must Up Bella Crearn Breast Enhance Cream, Liduoliya Breast Enhancement Frost, Breast Full Intensive Breast Enlargement Cream, Miracle Bust Cream, Eveline Slim Extreme 4D Intensive Serum.

  1. Allura (breast enhancement injections)

Maimakon shan kwayoyi ko kuma shafa mayuka na gyaran nono, wasu matan sukan yi allura a nononsu. Dalili shine ita allurar tana shiga cikin tsokar nonon ne kaitsaye domin ta bayar da tasirin da ake bukata. Allurai da ake amfani da su sun hada da Botox, Vampire Breast Lift Hyaluronic Acid (Ha)-based Dermal Fillers da sauransu.

Kuce Gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button