Labaran Duniya

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un; Wasu Mata Sun Watsawa Wani Saurayi Acid Kalli Wannan Bidiyon Domin Kaga Rashin Imanin..

Yusuf Kabiru yaro ne dan shekara 15 mazaunin Kofar Rini dake birnin Sokoto a Nigeria.

Yaro ne mai kwazo da kokarin Neman na kanshi inda yakeda shagon siyarda kayan abunci a unguwar su.

Wani abun bakin ciki wasu bata-gari da har yanzu ba’a san ko su waye ba suka watsa masa acid ga fuska inda har ya bata masa fuska da wani sashe na wuyan shi, inda hakan ya jefa shi cikin halin kaka-nikayi.

Mims Foundation ta samu zantawa da mahaifin shi inda ya bayyana mana cewa anyi iya kokari domin yi masa aiki a asibitin koyarwa ta Usmanu Dan fodio dake nan Sokoto (Uduth) domin ceto rayuwar yaron to amma saidai rashin Hali yasa sun kasa, inda asibitin suka tura su Kaduna domin yi masa aikin gyaran idanu, yayin da a can din aka nemi su biya naira miliyan daya (One Million Naira) inji mahaifin yaron.

Kamar yadda mahaifin yaron ya shaida mana Babu wani Wanda ya taimake su face sarkin fulanin Arkilla inda ya yaba masa tare da nuna jindadin sa ga kawainiyar da yayi dasu.

Shine muke Mika kokon barar mu wajen ‘yan-uwa Musulmai tare da kira ga masu hannu da shuni da ‘yan siyasa da mu-duba Allah mu taimaki wannan yaron domin ceto rayuwar shi.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button