Labaran Duniya

Tozarci Ne Biyan Naira Dubu Hamsin 50k A Matsayin Sadakin Aure Kalli Bidiyon Yadda..

Fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Shaikh Habibu Yahaya Kaura, ya ce sadaki shi ne ruhin aure, amma a yanzu zamani ya zo ba a daukarsa da muhimmanci.

Malamn ya ce a wannan zamani ana kashe makudan kudi wajen al’adun aure amma idan an zo kan sadaki sai a a tsuke bakin aljihu.

Sheikh Habibu Yahaya Kaura ya bayyana haka ne a wajen taron daurin auren ’ya’yan Babban Limamin Masallacin 1004, Sheikh Ibrahim Sulaiman, wanda aka yi a ranar Lahadin da ta gabata a cikin garin Legas.

Ya ce za ka ga idan auren mawadaci ne zai iya kashe Naira miliyan goma a al’adun da aka jingina wa aure, amma idan an zo kan sadaki sai ka ga an bayar da Naira dubu 50, alhali sadaki Musulunci ya shirya shi domin amarya ta samu abin da za ta yi hidima.

Ya ce shi sadaki ba na iyaye ba ne, hakkin amarya ce, yanzu sadaki akasari ko katifa ba ya saye.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button