Labaran Duniya

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un; Yadda Wata Mata Ta Kashe Mijinta Ta Hanyar Soka Masa Wuka

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Yadda Wata Mata Ta Kashe Mijinta ta kashishi da wuka kamar yadda a yanzu haka mutane da yawa Suna allah wadai da wannan matar.

Sunan ta Atika ‘yar Asalinta wani kauye ce Mai suna Kawari dake karamar hukumar Zango ta Jihar katsina suna zaune da mijinta A garin Mararaban Abuja da jihar Nasarawa.

Haihuwarsu Hudu da mijinta amma ‘daya ya rasu daga cikin ‘ya ‘yan su saura Uku yanzu, mijinta wanda ta kashe bakaniken mota ne sunan sa Ibrahim Ahmad, kusan watanni biyar da suka wuce ya Kara aure.

Kusan Shekara kenan da yayi Sabon gida Suka koma. Atika ta kasance mai tsananin kishi suna yawan yin fada da mijinta, anyi mata shedar masifa sosai, kuma kafin Ibrahim ta fara yin wani aure,

An ruwaito cewa shima tsohon mijinta na farko barazanar Kai farmaki take yawan yi masa da wuka hakan yasa ya rabu da ita, a baya ta ta6a yankan matar yayan mijinta da wuka a Lokacin da suke fa’da suna gida daya kafin mijinta yayi Sabon Gida su koma.

A yanzu haka wannan matar ta kashe Mijin ta kamar yadda a yanzu haka Duk wanda yaji Wannan Labarin sai yayi allah wadai da wannan matar domin bata da imani.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button