Duniya Tazo Karshe; Yadda Wani Matashi Ya Kashe Iyayen Sa Da Tabarya Kalli Video…

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un Gaskiya Ya Kama Aje Asibiti A binciki Kwakwalwar Wannan Matashi Domin wannan Abinda Ya Aikata Yayi Muni da Yawa.
Wani labari da mukai karo dashi mai ciem da al’ajabi cewa wani matashi da ya rankwala wa mahaifansa biyu tabarya ya kashe su, ya yi ikirarin cewa Jihadi ne abin da ya aikata.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa shi dai wannan matashi ya shaida wa ’yan sanda cewa ya yi amfani da tabarwa wajen kashe mahaifan nasa ne saboda izgili da suke masa idan yana yin ibada.
Kamar yadda muka kawo muku a baya Idan baku manta ba Aminiya ta kawo rahoton wanann abin al’ajabi da matashin ya hallaka mahaifiyarsa Hauwa, mai shekara 60 da mahafinsa Ahmad Muhammad, mai shekara 70, wanda kuma shi ne Daggacin kauyen Zarada-Sabuwa a Karamar Hukumar Gagarawa ta Jihar Jigawa.
Bai tsaya a iya kansu ba, domin sai da ya rankwala wa kishiyar mahaifiyarsa mai shekara 50, Hakilima Ahmadu tabaryar da kuma wani makwabcinsu, Kailu Badugu, wanda dattijo ne mai shekara 65.
Tuni dai mahaifan nasa suka ce ga garinku nan, amma an sallamo kishiyar mahaifiyarsa daga asibiti, shi kuma makwabcin nasu har yanzu yana kwance magashiyyan a asibiti.
Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu mai al’barka domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com