Kannywood

Tirkashi” Har Yanzu Ana Yayi Na A Masana’antar Kannywood Kalli Video Yadda Take Magana..

A wani labari na tattaunawa da tsohuwar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Fati Baffa Fagge, wacce a ke wa lakabi da Fati Bararoji.

Ta bayyana cewar ita fa har yanzu ba ta yi tsufan da za a daina yayin ta ba a cikin masana’antar, domin kuwa, har yanzu a na damawa da ita kamar lokacin kuruciyar ta.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin majiyar amihad.com jaridar Dimokuradiyya, dangane da har yanzu irin su da suka dade a harkar ba su matsu, sun bar wa yan baya ba, da suka shigo harkar a yanzu, kasancewar su jaruman da suka ci lokacin su a baya.

Sai dai Jarumar ta yi saurin bada amsa da cewar “Sam babu wani lokacin mu da za a ce mun ci a baya, kuma yanzu mun zo muna cin na wasu, domin babu wanda ya ke cin lokacin wani, don haka yanzu ma lokacin mu ne.” Inji ta.


Kuce gaba da bibiyar wannan shafin namu domin samun labarai masu ingance akoda yaushe Mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button