Labaran Duniya

Yan’ Jam’iyar APC Kawai Zan Marawa Baya A Zaben 2023; Shugaban Kasar Muhammadu Buhari Yayi Magana…

Babbar Magana Yanzu Yanzu Shugaban Kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana Wani Siri Akan Zaben 2023 kamar yadda ya kamata ka tsaya ka karan wannan labarin.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa mambobin Jam’iyyarsa ta APC kaɗai zai mara wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2023.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce ba zai goyi bayan tsofaffin ƴan APC ko ma ƴan siyasar da suka gurfanar da APC a gaban kotu ba.

Sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta ce “Buhari ya kasance soja mai ladabtarwa na APC kuma a zaɓen da ke tafe, zai mara baya ne kawai ga ƴan takarar Jam’iyyar.”

“Wannan gargaɗi ne ga ƴan jam’iyyar da suka sauya sheƙa da wadanda suka kai sahihan ƴan takarar APC kotu, su sani cewa ba ma tare da su kuma kar wani daga wajen Jam’iyyar da ya alaƙanta kansa da Shugaba Buhari.


A yanzu haka wannan Zaben na 2023 babu abinda zamuce sai sai muce allah ya bamu shugaban kasa na gari wanda zai tsaya domin Ya taimakawa talakawa kamar yadda mutane da yawa sun bayyana cewa wannan mulkin Basuji dadin sa ba.

Kuce gaba da bibiyar wannan shafin domin Samu labarin masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wanna shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button