Labaran Duniya

Acuci Mata: Amarya ta fasa Aure Ana Tsaka Da Daurin Aure Bayan Ta Ganon Angon Yana Da Sanko Akansa..

Kamar yadda ka sani dai a yanzu haka mutane da yawa Suna magana akan cewa mata da yawa Suna cewa baza su aure na miji mai sanko ba domin a yanzu haka Wani Abu mai ban mamaki ya faru.

babbar magana yanzu haka wata Amarya ta fasa auren Mijin daza ta aure bayan ta jano cewa wanda zata aura yana da sanko.

Bayan kwashe lokaci mai tsawo ana shirye-shiryen aure a kasar Indiya, amaryar ta kalli cewa ba za ta iya jure ganin kan angonta da sanko ba yasa ta fasa auren.

Dama idan aure ya matso, dayawa ana samun matsaloli, ko dai daga bangaren ango ko kuma amarya. Wani lokacin kuma daga duk bangarorin.

Lamarin ya faru ne gundumar Etawah da ke birnin Kanpur cikin Jihar Uttar Pradesh, wanda sankon ango ya zama sanadiyyar fasa auren.

Jaridar Times of India ta bayyana yadda hankali kwance ake tsare-tsaren yadda za a gudanar da bikin har ta kai ga ma’auratan sun yi musayar furanni.

An samu tangarda ne bayan amaryar ta kula da cewa angon ya yi nadin gargajiya akansa ne musamman don ya boye sankon da ke kansa.

Take a wurin ta bukaci wasu daga cikin tawagarta da su taimaka su bincika mata gaskiya idan sumar bogi ce a kansa ko kuma ta gaskiya.

Bayan gaskiya ta bayyana, amaryar ta shiga tashin hankali mara misaltuwa. Ta tambayi angon dakanta don sanin gaskiyar lamarin, amma ya bayyana mata cewa dagaske sanko ne akansa.


Kuce gana da bibiyar wannan shafin namu domin samun labarai masu ingance akoda yaushe mungode da ziyarar wannan shafin namu mai al’barka Digitalskil.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button