Shin Ko Kasan Zaka Iya Ajiye Lambobin Wayarka A FacebookShin Ko Kasan Zaka Iya Ajiye Lambobin Wayarka A Facebook

Shin Ko Kasan Zaka Iya Ajiye Lambobin Wayarka A Facebook

Assalamu Alaikum Warahamatullah, Barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na HikimaTv.Com

A yau nazo muku da darasi akan yadda zaku ajiye dukkan numbobin da suke kan wayarku akan facebook dinku cikin sauki.

Wannan hanyar zai baka damar copy numbobinka daga kan wayarka zuwa kan facebook naka koda kuwa sunkai 10,000 ba tare da ka rasa ko daya ba.

Dafarko Ka Tabbatar Kanada Facebook Account Tukun

Shin Ko Kasan Zaka Iya Ajiye Lambobin Wayarka A Facebook

Idan ya bude sai kayi can kasa ka shiga inda aka rubuta Settings

Shin Ko Kasan Zaka Iya Ajiye Lambobin Wayarka A Facebook

Sannan ka sakeyin kasa ka shiga Inda aka Rubuta Upload Contacts

 

Daga nan zakaga Inda aka rubuta Upload contacts Sai ka kunna shi

Daga nan zai kawo maka wani shafi saika danna inda aka rubuta Turn On

Daga nan zai sake kawo maka wani shafi wanda anan zakaga yana upload na dukkan number dake kan wayarka, saika jira ya gama upload din

Daga nan shikkenan ka gama dora dukkan lambobin da suke kan wayar ka.

Yanzu kuma sai yadda zakaga dukkan Lambobin daka dora a facebook din naka:

Shima Zaka sake shiga facebook din sai kaje setting sai ka kara shiga “Upload contact” bayan ya bude saika duba daga kasa zakaga rubutu blue inda aka rubuta “See contact you’ve uploaded in messenger”

Bayan ya bude sai ka duba daga kasa zakaga inda aka rubuta “See contact you’ve upload from facebook”

Anan ne zakaga dukkan jerin lambobin daka dora

ALLAH Yabada Sa’a

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*