HAUSA NEWS: Bayan dawowa daga Landan, hotuna sun nuna Buhari ya halarci zaman Tafsirin Al- Qur’ani



 

Bayan dawowarsa daga Landan inda ya tafi jinya, shugaba Muhammadu Buhari ya halarci zaman Tafsirin watan Ramadana a Masallacin fadar shugaban kasa, Aso Villa. Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya bayyana cewa Buhari ya halarci Tafisirin ne ranar Talata, 20 ga Afrilu, 2021. A cikin hotunan da ya saki, an ga shugaban kasa tare da hadimansa na jiki zaune cikin Masallaci tare da baiwa juna tazara don kariya daga cutar Korona. Daga cikin wadanda ke hallare akwai hadimi na Protocol, ADC, dss. Kamar yadda aka saba, Masallatai a fadin Najeriya sun kaddamar da Tafsirin Al-qur’ani cikin watan Ramadana.

Bayan dawowa daga Landan, hotuna sun nuna Buhari ya halarci zaman Tafsirin Al-Qur’ani Hoto: Femi Adesina Source: UGC 

Bayan dawowa daga Landan, hotuna sun nuna Buhari ya halarci zaman Tafsirin Al-Qur’ani Hoto: Femi Adesina Source: UGC

Bayan dawowa daga Landan, hotuna sun nuna Buhari ya halarci zaman Tafsirin Al-Qur’ani Hoto: Femi Adesina Source: UGC

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad, ya umurci daukacin al’ummar Musulmi su tashi da azumin watan Ramadana ranar Talata, 13 ga watan Afrilu, 2021.

Babban Malami, Shaykh Muhammad Bin Uthman, ya bayyana wasu fa’idoji 15 dake cikin wannan sabon wata da kuma ibadan da za’a gabatar a ciki. 


Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*