Rahotannisun bayyana kisan al’ummar Hausa a wani yankin jihar Imo da ‘yan Biafra suka yi – Sun hallaka Hausawa sama da 12, yayin da suka barnatar da dukiyar da ta haura mNaira miliyan 40 – Shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa, da sanin hukumomin tsaro hakan ke faruwa a yankin Rahotanni daga jihar Imo sun bayyana cewa mutum uku sun hallaka bayan wani hari da ake zargin Kungiyar mayakan Biafra ta kai wa al’ummar Hausawa da ke yankin Orlu a jihar ta Imo. Lamarin dai ya jefa al’ummar Hausawan da ke yankin cikin zaman zulumi. A cewar wani dan kasuwa Bahaushe mazaunin yankin na Orlu, Alhaji Amadu Ali, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu, kungiyar ta Biafra ta halaka Hausawa 12 baya ga asarar dukiya da suka tafka da haura ta kusan naira miliyan 42. “Mu dai mun tashi kawai ranar Laraba, wani mai nama, yana tafiya ya dawo da wuri kawai ya haɗu da wadannan mutanen suka bude masa wuta, suka sakar masa harsashi na AK47, nan take ya mutu”, in ji Alhaji Ahmadu Ali.
Yadda masu son ballewa a Najeriya suka kashe Hausawa 12 a Imo Hoto: dailypost.ng Source: UGC
Leave a Reply