HAUSA NEWS: Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gidan yari, Pantami 

Akwai yuwuwar gwamnatin Najeriya ta ɗaure duk ‘yan Najeriyan da ba su yi rijistar ‘yan ƙasa ba a gidan gyaran hali – Ministan sadarwa, Dr Ali Isa Pantami ya sanar da manema labaran cikin gidan gwamnati a Abuja cewa babu mara rijistar da zai sake morar romon damokradiyya – A cewarsa, gwamnati za ta tabbatar da wannan hukuncin bisa kundin tsarin mulkin Najeriya kuma zata tilasta yin rijistar akan kowa Za a ɗaure ƴan Najeriyan da suka ƙi yin rijistar ƴan ƙasa a gidan gyaran hali, don babu wanda zai mori romon damokradiyya ba tare da rijista ba a cewar ministan sadarwa, Dr Isa Pantami. Kamar yadda Channels TV ta wallafa, Pantami ya bayyana hakan a wani taro da suka yi na ministoci a gidan gwamnati dake Abuja. 

This has been qouted out of context. Pantami has not mentioned “14 years imprisonment.” But said NIMC has been 14 years in existence, since 2007. Since the session has been recorded by journalists. It is better to release the video for public to listen to it, please. Best wishes! https://t.co/2z3nr69vOw

— Isa Ali Pantami, PhD (@DrIsaPantami) April 1, 2021

 Ya bayyana yadda aka yanke shawarar ta ɗaure marasa rijistar inda yace hakan ya yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasar nan don kada wani mara rijista ya mori romon demokraɗiiyya. 

Yan Najeriya marasa lambar NIN zasu fuskanci hukuncin shekaru 14 a gida yari, Pantami. Hoto daga @Channelstv Source: Twitter 

Pantami ya nuna muhimmancin samun lambar rijistar don sadata da layukan wayar mutum da kuma sauran ayyuka da yanzu aka wajabta dole sai an haɗa da ita lambar katin. A cewar Pantami, baya ga ƙidayar yawan ƴan ƙasa, yin rijistar zai samar da yawan adadin ƴan Najeriya saboda tsananin muhimmanci. A cewar ministan fiye da ƴan Najeriya 51,000,000 ne suka riga suka yi rijistar kuma wajibi ne yin hakan. A wani labari na daban, Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya yi allurar riga-kafin cutar korona ta AstraZeneca. A watan Afirilun 2020, tsohon ministan ya kwatanta riga-kafin cutar corona da muguntar da za ta yi sakamakon mutuwar mililoyin jama’a. A watan Mayun 2020, yayin da ake ta cigaba da samar da riga-kafin cutar, tsohon ministan sufurin jiragen saman ya kushe wannan cigaba a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa an mayar da mutane “aladun turawa”.

Kuyi comment


Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*