HAUSA NEWS: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas 

Hare-haren makiyaya na baya-bayan nan a fadin yankin Igbo ya haifar da tashin hankali a yankin kudu maso gabas – Daruruwan mutane sun mutu saboda yawan hare-haren da makiyaya ke kaiwa manoma – Wata kungiyar mata a yankin ta bukaci hukuma data shawo kan hare-haren ko kuma su hau kan titi tsirara a duk fadin kasar Igbo Ndinne Igbo, wata kungiyar zamantakewar mata, ta yi barazanar cewa mambobinta za su yi tattaki tsirara a fadin kasar ta Igbo don nuna rashin amincewa da kashe-kashen da makiyaya ke yi a yankin idan har hukumomin da abin ya shafa ba su shawo kan lamarin ba. Yankin kudu maso gabas na fama da rikice-rikicen makiyaya a makwannin da suka gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Kungiyar ta yi Allah-wadai da harin makiyaya da ya auku a jihohin Enugu da Ebonyi, inda ta koka kan yadda yara ‘yan kabilar Ibo da dama suka zama cikin mummunan harin. Kungiyar a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jagoran ta, Misis Beatrice Chukwubuike, a ranar Asabar, 3 ga Afrilu kuma Legit.ng ta gani, ta yi kira ga shugabannin Najeriya da na Ibo da su kamo wannan mummunan lamarin kafin ya tabarbare.

Kashe-kashen makiyaya: Matan Ibo sun yi barazanar zanga-zangar tsirara a fadin kudu maso gabas Hoto: @MBuhari Source: Twitter 

A gefe guda, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista don yin addu’a ga hadin kan Najeriya da kuma dawowar zaman lafiya a kasar. A sakonsa na Ista ga ‘yan Najeriya, Atiku ya tuno da yadda kwayar cutar Coronavirus ta gurgunta harkoki sosai a yawancin kasashen duniya a shekara guda da ta gabata. Har ila yau tsohon Mataimakin Shugaban kasar, ya jinjina wa ma’aikatan lafiya wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen yaƙi da cutar. Source: Sarkiloaded.com.ng 

Upload Your Song


About Sarkiloaded 762 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*