HAUSA NEWS: Jami’an Tsaro Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Shi’a Almajiran Sheikh Zakzaky A Abuja 

Daga Bilya Hamza Dass

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja, sun bayyana cewa; Jami’an tsaro sun bude wuta kan ‘yan Shi’a Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky a yau Litinin.

Lamarin wanda majiya me tushe tace farmakin ya yi sanadin wani ‘Dan Shi’a 1 kuma ya raunata da yawa daga cikin su. Rahoton ya kara da cewa kuma Jami’an tsaro sun tafi da wasu daga ‘yan Shian.

Wani Shaidan da ya gani da ido ya shaidawa wakilin shafin Rariya cewa; “na fara ganin mutane Maza da Mata suna ta fitowa cikin layi suna rike da hotunan Zakzaky tare da manyan takardu da akayi rubutu a jiki sai yan sanda suka tare hany suka fara tsayar da su, bayan sunki tsayawa sai suka fara jefa Tiyagas daga nan kuma sai naji harbi da Bindiga sai mutane suka fara gudu” Inji shi.

SOURCE: Sarkiloaded

Upload Your Song


About Sarkiloaded 762 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*