HAUSA NEWS: Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Lakaɗawa Duka Har Suka Zubarwa Wani Haƙoransa 

Hotunan Alƙalan Wasa Da Fusatattun Ƴan Kallo Suka Yi Wa Duka Ciki Har Da Wanda Ya Rasa Haƙoransa. Hoto: @lindaikeji Source: Twitter

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa a kasar Ghana sun lakadawa alkalan wasa duka har sun cire wa wani hakori – Lamarin ya faru ne bayan an buga wasa tsakanin kungiyar Wanamafo Mighty Royals da Bofoakwa Tano a ranar 28 ga watan Maris – Magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidansu ba su gamsu da yadda alkalin ya hura wasan ba hakan yasa suka far masa bayan an tashi Fusatattun yan kallo sun lakadawa alkalan wasan kwallo duka a gasar wasar Division One a wasan da aka buga a mako na 14 a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, LIB ta ruwaito. A cewar kafafen watsa labarai na kasar Ghana, lamarin ya faru ne bayan da kungiyar Wanamafo Mighty Royals suka buga wasa da Bofoakwa Tano aka tashi wasan ba tare da an saka kwallo a ragar kowa ba.

Rahoton ya ce magoya bayan kungiyar da aka buga wasan a gidanta sun afka cikin filin bayan an hura usur din tashi suka lakadawa jami’an wasan duka har ta kai ga rafari Niatire Suntuo Aziz ya rasa wasu daga cikin hakoransa. A cewar Starr FM, maso kungiyar a gidanta ba su gamsu da yadda alkalin wasan ya yi aikinsa ba hakan yasa suka far masa da duka. 

Kamar yadda hotunan ya nuna, alkalan sun fita hayyacinsu sakamakon harin da yan kallon suka kai musu bayan wasan. 


Kuyi Comment anan

Mungode da ziyartar Wannan Shafin Sarkiloaded

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*