HAUSA NEWS: Gwamnatin Zamfara Zata Bada Tallafi Zunzurutun Kudi Naira Miliyan 50 Ga Yan Jahar Sokoto Wanda Wuta Tayiwa Barna



 

Daga El farouq jakada
Gwamnatin Zamfara zata bayar da tallafi kudi wanda suka kai darajar Naira miliyan 50 Ga ƴan kasuwar sokoton wanda iftila’in gobara babbar kasuwa ya shafa da kwanakin baya kadan.

Kamar yanda jaridar Channels ta ruwaito sanarwa ta fito daga bakin mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan wayar da kai da kuma harkar sadarwar wato Zailani Baffa yayi ziyarar jajantawa da ya wakilci gwamnatin ta Zamfara a gidan Gwamnatin sokoto.

“Abinda ya shafi sokoto tabbas muma Zamfara ya shafe mu saboda dole muyi kokarin mubada gudummawar mu”inji Gwamna Matawalle.

Sannan yabada uzurin Abinda ya hana su zuwa wannan jaje da wuri wanda ya bayyana bai wuce matsalar tsaron da jahar ta Zamfara ke fama dashi, inda ya karkare da neman taimako na Addu’ar sokotowa kan lamarin.

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*