HAUSA NEWS: Yan bindiga sun sace mutane 4 a Abuja, sun nemi a biya N200m kudin fansa 

An sake garkuwa da mutane a garin Kiyi da ke cikin Babban Birnin Tarayya – Wasu mutane dauke da makamai sun afkawa garin a ranar Laraba sannan kuma suka sace akalla mutane hudu – ‘Yan sanda sun ce suna nan kan bibiyar masu laifin da ke neman a biya su kudin fansa miliyan N200 Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba, 24 ga Maris, sun afka wa mazauna garin Kiyi da ke yankin Kuje na Babban Birnin Tarayya (FCT), inda suka sace a kalla mutane hudu, jaridar Daily Trust ta ruwaito. 


A cewar jaridar, wani Mista Salami Olalekan wanda ya kasance memba na ma’aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCTA) na cikin wadanda aka sace. 

Sarkiloaded ta samu labarin cewa William Salami, wani babban yayan wanda aka sacen, ya ce masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 200, miliyan 50 kan kowane mutum. Ya ce: “Masu garkuwar sun kira mu a waya, suna bukatar N50m kan kowane mutum”. An tattaro cewa ragowar mutane ukun da aka yi garkuwa da su hadar da wani direban tasi, dan acaba da kuma wani daban. An kuma ruwaito cewa ’yan bindigar sun shiga gidan daya daga cikin mutanen ta taga, tare da yin awon gaba da shi zuwa cikin daji.

Kakakin ’yan sandan birnin tarayya, Abuja, ASP Miriam Yusuf, ta tabbatar da sace mutanen, inda ta ce Rundunar na kokarin ceto su.

 A gefe guda, wasu yan bindiga sun farmaki yan sanda ya yin da suke sintiri a garin Ashaka, karamar hukumar Ndokwa ta gabas a jihar Delta. Yan bindigan sun caka ma ɗaya daga cikin yan sandan wuƙa wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa kuma suka jikkata wasu sannan suka babbaka ma motar da yan sandan ke sintiri da ita wuta. 

Aisha Musa ‘yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. 

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*