HAUSA NEWS: Rashin aikin yi cikin matasan Karkara ke rura wutan matsalar tsaro, Buhari 

Shugaba Buhari ya bayyana daya daga cikin abubuwan da ke rura wutan matsalar tsaro – Buhari ya yi kira ga masu hannu da shuni su taimakawa mutan Karkara – Buhari ya karbi bakuncin yan kasuwan taki a fadarsa dake Villa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin ayyukan yi cikin matasan Karkara ya zama babban kalubalen da ke rura wutan matsalar tsaro a Najeriya. Buhari ya bayyana hakan ranar Alhamis yayinda karban bakuncin kungiyar masu sarrafa taki a Najeriya (FEPSAN), rahoton DailyTrust. Shugaban kasan yace shekara da shekaru gwamnatocin da suka shude sun mayar da hankulansu kan raya birane maimakon raya Karkara. “A tsawon shekaru hudu da suka gabata, mun yi aiki tukuru domin daidaita abubuwa ta hanyar inganta aikin noma da bayar da kudade domin samar da ayyukan yi a Karkara,” Buhari yace.

“Yayinda muke kokarin fadada yunkurin tabbatar da tsaro da dakile matsalar tsaro, ya nada muhimmanci in bayyana cewa ba za’a samu dawwamammen zaman lafiya da cigaba ba sai mun hada kai wajen samar da aikin yi ga mutan karkara.” “Saboda haka ina kira ga gwamnoni, bankuna, da masu sanya hannun jari su rika shiga Karkara,” Buhari ya kara.

A bangare guda, Iyayen Leah Sharibu, ɗalibar da ‘yan Boko Haram suka sace a makarantar Dapchi a watan Fabrairu 2018, sun bayyana rashin kwato ta da shugaba Buhari ya yi da ‘Abun kunya’. Jaridar PM News ta ruwaito cewa iyayen sun yi wannan magana ne bayan rahoton da suka samu cewa Leah Sharibu ta sake haihuwa a karo na biyu. A wani saƙo da ya fitar a madadin iyayen ta, Dr Gloria Puldu, yace iyayen Leah Sharibu na roƙon gwamnatin Najeriya ta amince da taimakon ƙasar Amurka wajen ceto ɗiyar tasu.

 Source: Sarkiloaded

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*