NEWS: Yan Bindiga Sun Kashe Ma’aikatan Kwallejin Fasaha Ta Kaura Namoda Biyu a Zamfara 

A kalla mutane biyu aka kashe sannan aka sace guda a wani sabon harin a aka kai a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar Zamfara, TVC News ta ruwaito.

Wadanda aka kashe ma’aikata ne a Kwallejin Fasaha ta Kaura Namoda.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne suka kashe su a safiyar ranar Laraba.

Yan bindigan sun afka garin misalin karfe 2 na daren Talata amma mutanen garin suka fatattake su.

Sun sake dawowa bayan awanni biyu sun kashe mutum biyu daga nesa sannan suka sace wata mata.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce jami’ai sun bazama neman yan bindigan.

Sun yi kira ga jama’a su kwantar da hankulansu su cigaba da gudanar da harkokinsu tare da basu tabbacin cewa rundunar yan sandan za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na’abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*