NEWS: Masu Baburan Adaidaita Sahu Sun Shiga Yajin Aiki a Maiduguri 

Daruruwan masu baburan adaidaita-sahu da aka fi sani da Keke-Napep sun kauracewa tituna a Maiduguri sakamakon yajin aikin da suka fara kan abinda suka kira cin mutunci da jami’an gwamnati ke musu.

Fasinjoji da dama sun rasa abubuwan hawa zuwa wuraren da za su tafi yayin da yara yan makaranta suka rika takawa suna tafiya mai nisa domin zuwa makaranta, Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin direbobin a titin Baga, Usman Modu, ya ce direbobin suna biyan N100 na haraji a kullum, ‘amma idan aka jinkirta biyan zuwa wani lokaci sai a yi kari a kai matsayin tara idan kuma ka kasa biya sai a kwace makullin ka.

Suna cin mutuncin mu saboda tufafinmu, misali idan ka saka riga mara hannu toh ranan ba za a bari kayi aiki ba.

“Masu karbar harajin ma suna wuce gona da iri suna tambayan lasisin tuki wanda ba ya cikin aikinsu.”

Dukkan kokarin da aka yi na ji ta bakin jami’in karamar hukuma na gwamnatin jihar ya ci tura.

Wata daliba a Ibrahim Taiwo Estate ta ce ta yi tafiya mai nisa zuwa makaranta.

A wani labarin daban, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a ranar Litinin ta kama fitaccen mai wakokin yabon Annabi Muhammadu SAW, Bashir Dandago.

An kama shi ne kan zargin fitar da wakar da hukumar ta ce na iya tada fitina, da ta ce ya zagi malamai a jihar Kano kan matayarsu game da rikicin Sheikh AbdulJabbar Kabara.

Shugaban hukumar, Ismail Na’abba Afakallah ya tabbatarwa Daily Trust kamun.

Upload Your Song


About Sarkiloaded 762 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*