HAUSA NEWS: Gwamnatin Gombe Za Ta Gina Dakunan Karatu 110 A Makarantu 

Gwamnatin jihar Gombe za ta kashe naira miliyan 333 wajen gina dakunan karatu na zamani guda 110 a makarantun fadin jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da wani sabon dakin karatu a makarantar Firamare ta Jekadafari, da ke Gombe da kuma rarraba babura, da kayayyakin koyarwa dana wasanni ga makarantin da ke fadin jihar.

Kamar yadda sanarwar da babban daraktan yada labaran gwamnan na Gombe, Ismaila Uba Misilli ke cewa, Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya wakilta, ya shaida wa baki a wajen taron cewa gwamnatinsa ta gaji manyan kalubale a bangaren ilimi inda Gombe ta kasance ta 34 a jadawalin jihohi 36 na kasar nan a jarrabawar kammala sakandare, yana mai cewa hakan ne ma ya sa gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a wannan fanni, musamman a matakin farko domin ceto sashin daga durkushewa baki daya.

Ya kara da cewa, “Samar da dakunan karatun a makarantar firamaren wani mataki ne mai girma wajen magance kalubalen da ke tattare da ilimin firamare”.

Ya kara da cewa duba da muhimmancin dakunan karatu wajen karfafa gwiwar samun ilimi, ma’aikatar Ilimi ta jihar, ta hannun hukumar bunkasa ilimi daga tushe ta jihar SUBEB, za su gudanar da aikin gina dakunan karatu guda 110 masu inganci a fadin jihar akan jimillar kudi Naira miliyan 333 a matakin farko.

Gwamnan sai ya umarci Sakatarorin Ilimi da shugabannin makarantu a jihar su samar da lokacin shiga dakin karatu na akalla minti 80 a kowane mako don baiwa dalibai damar karatu da kansu karkashin jagorancin wani mai kula da dakin karatun.

Ya kara da cewa, “Gwamnati ta yi na’am da farin ciki ganin yadda aka sayi karin Babura 31 ga jami’an tabbatar da ingancin ilimi na ‘Quality Assurance’ a dukkanin Kananan hukumomi 11 na jihar domin inganta sa ido kan makarantun, tare da samar da kayayyakin koyarwa da kayan wasanni da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 85 hakan wani abun a yaba ne”.

Tun farko da ya ke jawabi, Kwamishinan Ilimi, Dauda Batari Zambuk ya ce manufofin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a  bangaren ilimi sun wuce tunani, yana mai bayyana hakan a matsayin sakamako wanda za a ci gaba da tunawa da shi tsawon shekaru masu zuwa.

Shugaban hukumar kula da ilimin bai-daya daga tushe ta jihaf, SUBEB, Hon. Babaji Babadidi ya ce a wani bangare na matakan inganta bangaren ilimi a jihar, gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta gudanar da gagarumin garambawul a jihar musamman a matakin farko.

Ya ce bikin kaddamarwar wani babban mataki ne da gwamnatin Inuwa Yahaya ta dauka na shigar da sabbin dabaru wadanda za su tabbatar da ingancin ilimin da ake bukata bayan ayyana dokar ta baci a bangaren.

Upload Your Song


About Sarkiloaded 762 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*