Babban jagora a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada gudunmuwan milyan 50 ga wadanda sukayi asarar dukiya a gobarar babbar kasuwar jihar Katsina. Channles TV ta rahoto cewa Tinubu ya sanar da hakan ne ranar Laraba yayinda ya kai ziyarar jaje ga gwamnatin jihar Katsina. Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar suka tarbe shi.
Kasuwar jihar Katsina ta ci bal-bal ne ranar Litinin inda akayi asarar dukiya na miliyoyin naira.
Leave a Reply