Sanatoci sun Amince da naɗa Kwamishinan Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin tarayya 

Majalisar dattijai ta amince da naɗin Wakil a matsayin kwamishinan hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya – Majalasar ta amince da naɗin nashi ne bayan duba rahoton Da kwamitin ta ya kawo a zaman majalisar na yau Talata. – Shugaban kwamitin Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana basu sami wata matsala ko laifi da shi wanda ake son naɗawa yayi ba. A ranar Talata, Majalisar dattijan ƙasar nan suka amince da naɗin Wakil Bukar a matsayin kwamishina a hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC). 

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan duba rahoton da kwamitin gudanar wa ya gabatar mata a zaman ta na yau Talata, kamar yadda Punch ta ruwaito 

Shugaban kwamitin Sen. Ibrahim Shekarau ya bayyana ma majalisar cewa wanda aka gabatar ɗin nada dukkan abubuwan da ake buƙata kafin naɗa shi. Ya ce kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya bayyana abubuwan da ake buƙata kafin naɗin wani a matsayin kwamishinan FCSC a sashi na 156. Shekarau ya ce: “Babu wani rahoton tsaro da yazo gaban kwamitin a kan wanda akeson naɗawa kwamishina a hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC).” “Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar yan sanda sun kawo ma kwamiti rahoton rayuwar wanda akeson naɗawa har zuwa yau, kuma rahoton bai nuna wani laifi na tsaro da yayi ko aikata ba dai-dai ba.” inji Shekarau. “Kuma har zuwa yau ba’a kawo ma kwamiti ƙarar wanda ake son a naɗa ba” inji shi. 

“Kamar yadda doka ta tanadar, kwamiti ya tabbatar da cewa wanda ake son naɗawa a muƙamin kwamishina na hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya ya cancanta,” inji shekarau. Daga nan ne sai majalisar ta tabbatar da naɗa Wakil Bukar a matsayin kwamishinan hukumar FCSC. 

Shugaban hafsun sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce dakarunsa sun kammala shirin ganin bayan ‘yan bindigan da ke kawo rashin zaman lafiya. Da yake magana wajen taron da aka shirya a Abuja a kan sha’anin tsaro, Janar Lucky Irabor, ya ce za su bankado duk wadanda su ka fake a jeji su na ta’adi.

Upload Your Song


About Sarkiloaded 763 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*