Hausa News: Wasu Ƴan Bindiga Da Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Kai Hari Ga Tawagar Samuel Ortom Gwamnan Jahar BenueWasu fusatattun ƴan bindiga sun kaiwa gwamna Benue wato Samuel Ortom hari a hanyar sa ta Makurdi/Gboko dake karamar hukumar mulki ta Makurdi, a ranar Asabar.

Jaridar channels ta tattauna da wani makusanci Gwamnan inda ya bayyana yanda lamarin ya faru dasu a hanyar su a yayin Kaddamar da harin.

“yan bindigar akalla zasu kai su goma sha biyar kuma sun fito ne ta gefen wani kogi inda muka gansu ba zato ba tsammani” inji shi.

Saidai jami’ai namu tuni suka yinƙuro domin bawa Gwamnan kariya ta musamman inda har mukayi nasarar barin gun dashi batare da ko ƙwarzane ba.

Daga Kasim Ibrahim (Brabis)

Upload Your Song


About Sarkiloaded 762 Articles
Sarkiloaded Owned By Dj LaMszXy Got Team With Kasim Ibrahim As Best Blogger We Offer The Followings Music Promotion | Video Promotion | Dj Mix Promotion News | Advertise | Online Media

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*